Babban sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon ya yi ganawa tare da ministan tsaron kasar Isra'ila Moshe Ya'alon a hedkwatar majalisar da ke New York a ranar 20 ga wata, inda ya jaddada cewa, yana da muhimmancin gaske ga bangarori biyu wato Palestinu da Isra'ila da su maido da shawarwari tsakaninsu.
Yayin ganawarsu, Ban Ki-moon ya ce, idan ana son warware matsala tsakanin Palestinu da Isra'ila, yana da muhimmancin gaske gare su da su sake komawa teburin shawarwari nan take ba tare da bata lokaci ba.
Mr. Ban ya nuna yabo ga goyon bayan da Isra'ila ke samarwa wajen sake gina zirin Gaza ta hanyar kafa wani tsari na wucin gadi, kuma yana fatan Isra'ila za ta ci gaba da yin kokari kan wannan batu.
Ban da haka, Mr. Ban ya bayyana cewa, yana shirin kafa wani kwamiti na musamman domin yin bincike kan batun da ya shafi gine-ginen majalisar dake zirin Gaza wadanda hare-haren Isra'ila suka lalata a yayin rikicin kungiyar Hamas da Isra'ila a cikin 'yan kwanakin da suka gabata. (Jamila)