in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe kimanin 60 sun mai da martani ga tsarin "zirin da hanyar siliki ta ratsa da hanyar siliki ta kan teku" da Sin ta fitar
2015-03-23 20:41:38 cri
A yau Litinin 23 ga wata, ministan harkokin waje na Sin Wang Yi ya yi jawabi a gun babban taron dandalin tattaunawar bunkasuwa ta Sin a shekarar 2015 inda yace, a yayin da ake fuskantar manyan kalubalolin duniya, Sin ta yi tayin kafa sabuwar dangantakar kasa da kasa da ake fi mai da hankali a kan hadin gwiwa da juna da samun moriyar juna, tare da bukatar bayyana wannan ra'ayi a fannoni daban daban na yin hadin gwiwa da kasashen waje, kamarsu siyasa, tattalin arziki, tsaro, al'adu da sauransu.

Wang Yi ya bayyana cewa, gwamnatin Sin ta yi kokarin sa kaimi ga gudanar da wannan tsari na bunkasa zirin da hanyar siliki ta ratsa da hanyar siliki ta kan teku cikin karni na 21, ba kawai ne da zummar tayar da tunanin hanyar siliki ta gargajiya ba, har ma da niyyar yin hadin gwiwa da kowa ke bukata a yanzu. A sabili da haka, kasashe daban daban kimanin 60 sun riga sun mai da martani kan shiga wannan aiki.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China