Zhang ya ce, a cikin sabon yanayin da Sin ke ciki, samun ci gaba babban tushe ne na warware dukkanin matsalolin da ake fuskanta. A sabili da haka, dole ne a tsaya tsayin daka kan neman samun bunkasuwa.
Bayan haka, Zhang ya jaddada cewa, dole ne mu bi tsarin samun bunkasuwa a fannoni hudu, mu samu daidaito da jagoranci cikin sabon yanayi na raya tattalin arziki, a kokarin bude sabon babi na bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasa a wannan sabon matsayi na tarihi.
Sin ta yi tayin kafa zirin tattalin arziki da hanyar siliki ta ratsa da hanyar siliki kan teku cikin karni na 21 tare, kuma ta yi kira da a kafa bankin zuba jari na Asiya da asusun hanyar siliki, tare da samun amincewar kasashe da yawa. Ana maraba da masu zuba jari daga kasa da kasa da su shiga aikin bunkasa "zirin siliki da hanyar siliki", domin su yi hadin gwiwa da juna da samun moriyar juna, a kokarin samar da makoma mai kyau a nan gaba.(fatima)