Mr. Gao ya bayyana hakan ne a gun taron dandalin tattaunawa kan raya kasar Sin a jiya Lahadi, yana mai cewa duk da yawan jarin da kasashen duniya suka zuba kai tsaye a shekarar 2014 ya ragu da kashi 8 cikin dari, kasar Sin ta kara yin amfani da jarin ketare, kuma yawan irin wannan jari ya kai matsayin farko a fadin duniya.
Har wa yau Mr Gao ya bayyana cewa, a karkashin halin sabon tsarin yau da kullum na kasar Sin, gwamnatin kasar Sin za ta yi amfani da aikin gina muhalli, da dokoki, da tsari da manufofi da dai sauransu, don kara yin amfani da jari daga kasashen ketare.
Ya ce manufofin Sin na bana a wannan fanni sun hada da sassauta shigar da jari, da samar da kasuwannin da bangarorin ketare suka zuba jari a cikin kasar, da kara bude kofa ga kasashen waje kan sha'anin bada hidima, da na kera kayayyaki. Sauran sassan sun hada da kyautata tsarin sa ido ga kasashen waje wajen zuba jari, da tsarin bincike kan jarin, domin inganta zuba jarin da 'yan kasuwa na ketare ke yi yadda ya kamata, da kuma gyara dokokin dake shafar zuba jarin, da tsara dokar zuba jari da kasashen waje ke yi. (Zainab)