in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sassan duniya daban daban na juyayin rasuwar tsohon firaministan Singapore
2015-03-23 15:44:03 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jajantawa shugaban kasar Singapore Tony Tan Keng Yan ta wayar tarho, game da rasuwar Lee Kuan Yew, mutumin da ya bayyana rasuwarsa da babban rashi ga jama'ar kasar Singapore da ma gamayyar kasa da kasa.

Kaza lika firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya bayyana jajensa ga takwaransa na kasar Singapore Lee Hsien Loong ta wayar tarhi a yau Litinin din nan.

A daya bangaren kuma, shugaban kasar Amurka Barack Obama ya fidda wata sanarwa, wadda ke dauke da sakon ta'aziyyar rasuwar tsohon firaminista Lee Kuan Yew.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China