Lee Kuan Yew ya taimakawa kyautata hulda tsakanin Singapore da Sin, in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Sin, mista Hong Lei, ya fidda wani sharhi game da rasuwar tsohon firaministan kasar Singapore Lee Kuan Yew, inda ya bayyana Lee Kuan Yew a matsayin mutumin da ya aza harsashin kafuwar huldar dake tsakanin kasashen Sin da Singapore, matakin da ya ba da gudunmowa sosai ga kokarin kyautata wannan hulda.
Saboda haka ne a cewar Mr. Hong kasar Sin ke matukar bakin ciki game da rasuwar mista Lee. Kaza lika a madadin al'ummar kasar Sin da gwamnati, Mr. Hong ya mika jaje na musamman ga gwamnati da jama'ar kasar Singapore, gami da iyalan marigayi Lee Kuan Yew. (Bello Wang)