in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
IS: Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da kisan Misirawa
2015-02-17 11:40:57 cri

Da babbar murya babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da kisan wasu kiristoci Kibdawa su 21 da dakarun reshen kungiyar IS da ke kasar Libiya suka yi.

Ban wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ofishinsa ya fitar, ya nuna matukar takaicinsa game da kisan Misirawan bisa dalili na addini. Mr. Ban ya kuma jajanta wa iyalan mutanen da ma gwamnatin kasar Masar. Ya sake nanata cewa, sabon zagayen shawarwarin da kasar Libiya ke yi, zai ba da kyakkyawar damar kawo karshen rikicin kasar. Ta hanyar shawarwari ne kawai jama'ar kasar ta Libiya za su iya kaiwa ga kafa hukumomin kasa da ka iya yakar ta'addanci.

A wani ci gaban kuma, firaministan gwamnatin wucin gadi ta Libiya Abdullah Al-Thani, ya yi kira ga kasashen duniya da su kara dakile ayyukan kungiyoyin 'yan ta'adda dake kasar. Kalaman firaministan dai na zuwa ne bayan da sojojin saman kasar Masar suka yi luguden wuta kan dakarun kungiyar IS dake kasar ta Libiya.

A daya hannun kuma, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar Abdulaati ya ce, yanayin tsaron da kasar Libiya ke ciki, na barazana ga zaman lafiya da tsaron dukkanin duniya, don haka a cewarsa, ya kamata masu ruwa da tsaki musamman ma kwamitin sulhun MDD, su hada kai da kasar Masar, wajen sauke nauyin dake wuyansu na tallafawa yakin da ake yi da ayyukan ta'addanci.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China