in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi shirin harba kumbuna sau 20 zuwa sararin samaniya a shekarar 2015
2015-03-17 20:59:39 cri

A yau ne hukumar binciken sararin samaniya ta kasar Sin ta sanar da cewa, kasar Sin ta yi shirin kammala ayyukan harba kumbuna zuwa sararin samaniya har sau 20 baki daya a shekarar 2015 da muke ciki, wanda ya karya matsayin bajinta a tarihin kasar, inda kuma za ta harba kambuna fiye da 40 zuwa sararin samaniya, yawan kumbunan da shi ma ya karya matsayin bajinta a tarihin kasar ta Sin.

Zhao Xiaojin, shugaban sashen binciken sararin samaniya na hukumar binciken sararin samaniya ta kasar Sin ya yi bayani cewa, dalilan da suka sa kasar Sin za ta iya harbar kumbuna masu yawan haka kuma har sau 20 zuwa sararin samaniya a bana su ne, da farko kasar Sin ta inganta kwarewarta sosai wajen kera kumbuna da kuma rokoki masu dauke da kumbuna, na biyu kuma, tana amfani da filayen harba kumbuna yadda ya dace, na uku kuwa, kasar Sin ta warware matsala ta fuskar harba kumbuna a lokacin hunturu. Mista Zhao ya fayyace cewa, kasar Sin za ta harba dakin gwaje-gwaje na Tiangong-2 zuwa sararin samaniya a lokacin da ya dace a shekarar 2016, yayin da za ta fara shirin harba kumbon Chang'e-5 a farkon shekarar 2017. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China