Tun da farko dai da karfe 8 da minti 26, 'yan saman jannatin suka sarrafa wasu na'urori dake kumbon, don sanya kumbunan 2 rabuwa da juna, bayan haduwarsu ta farko wadda aka aiwatar da na'ura mai kwakwalwa, sa'an nan kumbon Shenzhou-10 ya janye jiki zuwa wani wuri maras nisa da Tiangong-1. Daga bisani kuma, bayan da cibiyar sarrafa kumbuna dake birnin Beijing ta tabbatar da yanayin da kumbunan 2 ke ciki, dan saman jannati mai suna Nie Haisheng, ya sarrafa wata na'ura dake cikin Shenzhou-10, domin matsar da shi kusa da Tiangong-1, yayin da ragowar abokan aikinsa Zhang Xiaoguang, da Madam Wang Yaping ke kallon gudanar wannan aiki, na sake haduwar kumbunan 2 ba tare da wata matsala ba.
Da karfe 10 ne dai kumbunan 2 suka fara taba juna. Kana zuwa karfe 10 da minti 7, aka kammala aikin hada su. Bisa ajandar aikinsu, 'yan saman jannatin 3 za su sake shiga cikin kumbon Tiangong-1, don kara gudanar da wasu gwaje-gwajen kimiyya da fasaha. (Bello Wang)