in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kumbon Shenzhou-10 ya sauka kasa cikin nasara
2013-06-26 08:48:05 cri

Ranar Larabar nan 26 ga wata ne da karfe 8 da 'yan mintuna bisa agogon Beijing, kumbon Shenzhou-10 mai dauke da 'yan sama jannati 3 ya sauka a wani yankin mai ciyayi dake jihar Mongoliya ta gida ta kasar Sin, kamar dai yadda tun da fari a aka shirya. An kuma tabbatar da cewa, 'yan saman jannati 3 dake cikin kumbon suna cikin koshin lafiya.

A ranar 11 ga wata ne dai aka harba kumbon Shenzhou-10 zuwa sararin samaniya. Bayan da ya yi kwanaki 2 yana shawagi, kumbon ya hada jikinsa da wani kumbon na daban mai suna Tiangong-1 bisa jagorancin na'ura mai kwakwalwa. Zuwa ranar 20 ga wata, 'yan saman jannatin dake cikinsa sun shiga kumbon Tiangong-1 don gudanar da wasu gwaje-gwajen kimiyya da fasaha, gami da koyar da darasi ga yaran kasar Sin. Sa'an nan a ranar 23 ga wata, an sake hada jikunan kumbunan 2 bisa sarrafawar 'yan saman jannatin.

Har ila yau a ranar 24 ga wata, shugaban kasar Sin Mista Xi Jinping ya yi hira da 'yan saman jannatin ta wasu na'urorin sadarwa. A kuma ranar 25 ga wata, 'yan saman jannatin 3 sun bar kumbon Tiangong-1 don komawa kumbon Shenzhou-10, sa'an nan suka raba jikunan kumbunan 2 wadanda suke a hade a wannan lokaci, sa'an nan suka sarrafa Shenzhou-10 don ya zagaya Tiangong-1 gami da sake haduwa da shi. A karshe, a ranar Larabar nan 26 ga wata, kumbon Shenzhou-10 ya komo gida, kuma ya sauka kasa lami lafiya. (Bello Wang).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China