in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da 'yan saman jannati da masu binciken kimiyya da fasaha na kasar Sin
2013-07-27 16:40:57 cri

Shugaban kasar Sin mista Xi Jinping a ranar Jumma'a 26 ga wata ya gana da 'yan saman jannati da suka tuka kumbon Shenzhou mai lamba 10 wajen shawagi a sararin sama, da wasu sauran masu binciken kimiyya da fasaha da suka ba da gudunmowa a gwaje-gwajen da suka gudanar cikin kumbon Shenzhou, a babban dakin tarukan jama'ar kasar Sin dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar.

Shugaban ya jinjina wa 'yan saman jannatin da masu binciken kimiyya da fasaha, gami da jaddada cewa, nasarorin da aka samu a kokarin harba kumbuna masu daukar mutane sun nuna karfin kasar Sin da daidaitacciyar turbar raya kanta da kasar ta dauka, saboda haka sun karfafa gwiwoyin al'ummar a kokarin cika burinsu na farfado da kasar da kara ciyar da ita gaba.

A cewar shugaba Xi, yadda aka kammala aikin harba kumbon Shenzhou mai lamba 10, ya sheda babban ci gaban da aka samu ta fuskar ayyukan harba kumbuna masu dauke da mutane a kasar Sin, wanda ya kasance wani mihimmin sakamako ne da aka samu bayan shekaru 21 da aka kwashe ana kokarin raya fasahohin kumbuna masu dauke da mutane a kasar Sin.

An harba kumbon Shenzhou mai lamba 10 a ranar 11 ga watan Yuni da ya gabata, sa'an nan an dawo da shi gida a ranar 26 ga watan.

Yayin da kumbon ke shawagi a sararin sama, ya hada jikinsa da kumbon Tiangong mai lamba 1 har sau 2, daya karkashin kulawar kwamfuta, dayan kuma bisa sarrafawar 'yan sama jannatin. Gwaje-gwajen da aka gudanar sun tabbatar da ci gaban fasahar hada kumbuna ta kasar Sin. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China