in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An harba kumbon Shen Zhou -10 cikin nasara
2013-06-11 20:25:38 cri

A ranar 11 ga wata da karfe 5 da minti 38 na yamma bisa agogon Sin ne, aka harba kumbon Shen Zhou mai lamba 10 dauke da 'yan sama jannati 3 daga cibiyar harba kumbo dake garin Jiuquan na lardin Gansu na kasar Sin. Daga bisani, kumbon ya kama hanya zuwa sararin sama kamar yadda aka tsara kuma akan lokaci. Lamarin da ya sheda cewa, an harba kumbon cikin nasara.

'Yan sama jannati maza 2 wato Nie Haisheng da Zhang Xiaoguang, gami da mace daya mai suna Wang Yaping, za su yi kwanaki 15 suna gudanar da wasu ayyuka a sararin samaniya. A tsawon wannan lokaci, wanda shi ne mafi tsawo a tarihin zirga-zirgar kumbon kasar Sin a sararin samaniya, kumbon Shen Zhou mai lamba 10 zai hade da kumbo Tian Gong mai lamba 1 dake shawagi a sama a karo 2 a waje guda, bisa jagorancin na'ura mai kwakwalwa, da kuma sarrafawar 'yan sama jannatin.

Yayin da ake hade kumbon Tian Gong mai lamba 1 da na Shen Zhou mai lamba 10, 'yan sama jannatin 3 za su shiga kumbon Tiang Gong mai lamba 1 don gudanar da gwaje-gwaje masu alaka da aikin likita, da wasu sauran fasahohi, gami da koyar ma dalibai darassi daga sararin samaniya.

A cewar Zhou Jianping, babban jami'in da ya kirkiro kumbon da ke daukar mutane zuwa sararin samaniya na kasar Sin, kumbon Shen Zhou dake hade da roka sanfurin Chang Zheng-2F, sun kasance wata dabarar kai mutane da kaya zuwa can sama da dawowa da su gida kawai da ake samu a halin yanzu, baya ga kumbon Soyuz na kasar Rasha. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China