A ran 24 ga watan Oktoba na bana ne aka harba wannan kumbon gwaji a cibiyar harba taurarin dan Adam dake Xichang na kasar Sin, daga bisani ya kama hanyar zuwa duniyar wata. Daga karshe dai, kumbon ya dawo kuma ya sauka a wurin da aka tsara kamar yadda ake fata a ran 1 ga watan Nuwamba. Wannan ya nuna cewa, an samu nasarar wannan gwaji matuka.
Bisa shirin da aka tsara, ya zuwa shekarar 2017, kasar Sin za ta harba wani kumbo samfurin Chang'e mai lamba 5 maras matuki zuwa duniyar wata, sannan zai dawo duniyarmu da samfurin da ya samo a duniyar wata. (Sanusi Chen)