in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta yi gwajin harba wani kumbo zuwa sararin samaniya
2014-10-24 15:39:45 cri

A yau Juma'a ne kasar Sin ta yi gwajin harba wani kumbo maras matuka, wanda kuma aka tsara domin gudanar da gwaje-gwaje na fasahohi da za'a yi amfani da su cikin na'urar binciken duniyar wata mai nau'in Chang'e- 5 a nan gaba da zimmar komo duniyarmu daga duniyar wata bayan binciken a karo na farko.

Gaba dayan wannan shirin zai dauki kwanaki 8, kuma kumbo zai je ya zagaya rabin zagayen kusa da wata, kafin ya dawo nan duniya.

An harbi kumbon ne daga cibiyar harbar tauraron dan adam ta Xichang dake yankin Sichuan a kudu maso yammacin kasar Sin.

Wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta kaddamar da irin wannan gwaji, inda kuma ya shafe kilomita dubu 380 kafin ya dawo nan duniya daga duniyar wata. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China