in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar likitoci ta mataki na 4 ta lardin Shaanxi na kasar Sin ta tashi zuwa Afrika
2015-03-16 15:20:11 cri

Kamfanin dillancin labaru na Xinhua a kasar Sin ya samu labari daga kwamitin kiwon lafiya da kayyade iyali na lardin Shaanxi na kasar a yau Litinin cewa, tawagar likitoci ta lardin ta mataki na 4 da ta kunshi membobi 16 sun tashi daga birnin Guangzhou jiya domin ba da taimakon jinya ga kasar Malawi, wadda wa'adinta zai kai shekaru biyu.

Daga cikin wadannan likitoci 16, akwai kwararrun likitoci masu matsayin darekta biyu, kana da masu matsayin mataimakin darekta 9, dukkansu sun kasance fitattun likitoci masu kwarewa a asibitocinsu.

Kasar Malawi ta kasance a kudu maso gabashin nahiyar Afrika, wadda ke fama da rashin kwararru a fannin kiwon lafiya, kuma jama'arta na fama da cutar kanjamau da zawaye da kuma sauran cututtuka masu yaduwa.

Wani jami'in kwamitin kiwon lafiya da kayyade iyali na lardin Shaanxi na kasar Sin ya tabbatar da cewa, domin gudanar da aikin jin kai, kasar Sin ta tura tawagar likitoci ta farko daga lardin Shaanxi zuwa kasar Sudan a shekarar 1971. A cikin shekaru fiye da 40 da suka gabata, yawan likitoci da masu aikin jinya da lardin Shaanxi ya tura wa kasashen Sudan, Malawi da Vanuatu da kuma sauransu ya kai fiye da dari 9.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China