in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar Malawi ta sanar da sabbin ministocinta
2013-10-16 10:49:14 cri

Shugabar kasar Malawi Joyce Banda ta sanar da sunayen sabbin ministocinta bayan ta rushe tsoffin 'yan majalisar zartaswar kasar a makon da ya gabata sakamakon zargin da ake musu na cin hanci da rashawa.

A ranar Talata 15 ga wata ne shugabar ta sanar da sabbin ministocin nata, inda canjin ya yi awon gaba da ministan kudi Ken Lipenga, da na shari'a da kuma ministan kula da harkokin da suka shafi doka Ralph Kasambara.

Tun a watan Satumba ne dai ake ta damke jami'an gwamnatin da ke aiki a baitul malin kasar, akanta janar da wadanda ke aiki a ofishin shugaban kasa da majalisar zartaswar kasar da ake zargi da hannu a badakalar miliyoyin daloli.

Kafin ta rushe majalisar ministocin a ranar Alhamis, shugaba Banda ta fuskanci matsin lamba kan ta kori ministanta na kudi domin a samu kafar gudanar da bincike cikin adalci. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China