in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar DPP ta gaza samu rinjaye a kujerun majalisar dokokin Malawi
2014-06-04 09:34:37 cri

Rahotanni daga kasar Malawi na cewa, jam'iyyar DPP wadda ta lashe zaben shugaban kasar da ya gabata ran 20 ga watan Mayu, ba ta samu cikakken rinjaye a kujerun majalissar dokokin kasar ba.

Wannan rashin rinjaye da jam'iyyar ta DPP ta ci karo da shi a majalissar dokokin kasar dai na nuni da cewa, dole ne ta hada kai da wasu daga jam'iyyun adawa, wajen tabbatar da nasarar kowane irin kuduri da za a gabatar a zauren majalissar.

Kididdigar kujerun majalissar dokokin kasar wadda hukumar zaben kasar MEC ta fitar a baya bayan nan ta nuna cewa, jam'iyyar DPP ta sabon shugaban kasar ta lashe kujerun majalissar guda 50 cikin kujeru 192, yayin da jam'iyyar shugabar kasar mai barin gado ta PP ta samu kujeru 26. Ragowar jam'iyyun da ke kan gaba a yawan kujerun wakilcin sun hada da MCP mai kujeru 48, da kuma UDF wadda ta samu kujeru 14, akwai kuma 'yan takara masu zaman kansu da suka samu kujeru 52.

Haka nan cikin jimillar kujerun wakilcin majalissar 'yan takara mata sun lashe kujeru 30. An kuma ware mako guda ga daukacin 'yan takara masu korafi da su gabatar da kokensu, ga babbar kotun kasar domin daukar matakai na shari'a.

Kafin hakan dai hukumar zaben ta MEC ta bayyana sunan Peter Mutharika a matsayin mutumin da ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasar ta Malawi, bayan da ya samu kaso 36 bisa dari, na daukacin kuri'un da aka kada. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China