in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar hukumar zartaswar kungiyar AU tana kasar Malawi
2014-05-15 09:59:10 cri

A ranar Laraba ne shugabar hukumar zartaswar kungiyar AU madam Nkosazana Dlamini Zuma ta isa birnin Blantyre na kudancin kasar Malawi gabanin zaben kasar da aka shirya gudanarwa a ranar 20 ga watan Mayu.

Wata sanarwa da kungiyar AU ta bayar, ta bayyana cewa, madam Zuma za ta hadu da Sam Nujoma, tsohon shugaban kasar Namibia, kana shugaban tawagar AU da ke sa-ido kan zaben kasar (AUEOM) da 'yan tawagarsa, inda za su bayyana goyon bayansu ga al'ummar kasar ta Malami na ganin an gudanar da zabukan kasar Malawi, da ma nahiyar baki daya cikin gaskiya da adalci.

A yayin ziyararta a kasar ta kwanaki uku, madam Zuma za ta ziyarci shugaba Joyce Banda, tare da gana wa da shugabannin sauran jam'iyyun siyasa da ke takara a zabukan kasar.

Tun a ranar 12 ga watan Afrilu ne aka tura tawagar sa-ido mai wakilai 10 zuwa kasar, wadda aka hade ta da sauran wakilai 40 din da ta kunshi tawagar AUEOM a ranar 13 ga watan Mayu. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China