in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sake kirga kuri'un zaben Malawi zai kwashe kwanaki 30
2014-05-27 10:33:41 cri

Hukumar gudanar da zaben kasar Malawi MEC, ta ce, aikin sake kirga kuri'un zaben kasar da aka gudanar ran 20 ga watan nan, zai kammala nan da kwanaki 30 masu zuwa. Kasancewar a yanzu haka ta fara amfani da hanyar kidaya ta hannu domin sake lissafta kuri'un.

A cewar shugaban hukumar ta MEC Maxon Mbendera, an tsai da kidayar kuri'un a baya ne, domin samar da damar sake kidaya kuri'un wuraren da ake zargin an tafka magudi. Ya ce, akwai bukatar jam'iyyun kasar su gabatar da manyan wakilansu yayin wannan aiki na sake kidayar kuri'un.

Zaben dai na Malawi ya sha suka, inda wasu masu ruwa da tsaki ke cewa, an tafka magudi a cikin sa, ga karancin kayan aiki a wasu wurare, baya ga adadin kuri'u da bai yi daidai da yawan masu kada kuri'un a wasu yankuna ba.

Kafin hakan dai shugaba Joyce Banda ta ba da sanarwar soke zaben, tare da ba da umarnin sake sabo cikin kwanaki 90, matakin da ya sha suka daga masanan shari'a da dama.

Wannan ne dai karon farko da aka gudanar da zaben shugaban kasar ta Malawi, da na 'yan majalissu, da kuma na wakilan kananan hukumomi a rana guda. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China