Shugabar kasar Malawi Joyce Banda a yammacin ranar Alhamis din nan 10 ga wata ta sanar da rusa majalissar ministocinta, ganin yadda ake ta zargin magudi da cin hanci a gwamnatinta.
Wannan al'amari ya biyo bayan yawan kame na manyan da kananan jami'an gwamnati da ake yi ta yi wadanda aka same su dumu dumu da miliyoyin dalar Amurka a gidaje da kuma cikin motocinsu.
Korafin 'yan adawa da kungiyoyi masu zaman kansu a kan ko dai shugabar za ta sauka daga mukaminta ko kuma za ta kori ministan kudinta da babban magatakardarta, ya sa tana dawowa daga babban taron MDD a birnin New York a ranar Laraba, ta shaida wa manema labarai a Blantyre, birni na biyu mafi girma kuma cibiyar kasuwancin kasar, cewa za ta dauki matakin da ya kamata bayan ta gana da 'yan majalissar nata a ranar Alhamis.
Wata majiya da ba'a tabbata ba na nuna cewa, wadansu ministoci na hannun daman shugabar na cikin wadanda ake zargi da ayyukan magudin da cin hanci da ya jefa al'ummar kasar cikin wani hali mai tsanani.
Ana dai sa ran shugaba Banda ta sanar da sabuwar majalissar ministocinta nan ba da dadewa ba. (Fatimah)