in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sauke sakataren gwamnatin kasar Malawi daga mukaminsa
2013-03-12 11:05:56 cri

Shugabar kasar Malawi Joyce Banda, ta sauke sakataren gwamnatin kasarta Bright Msaka daga mukaminsa, jim kadan bayan tsafke shi, tare da wasu tsofaffin ministocin kasar su 7, da wasu jami'an gwamnati 2, bisa zargin da aka yi musu na boye gaskiya, don gane da rasuwar tsohon shugaban kasar ta Malawi Bingu Mutharika.

Cikin mutane goman da aka tsare ran Litinin 11 ga wata. bisa wannan zargi, akwai tsohon shugaban jam'iyyar siyasar kasar ta DPP, da tsohon ministan harkokin wajen kasar Peter Mutharika, da kuma ministan tsara harkokin tattalin arziki da samar da ci gaba Goodall Gondwe.

Wani rahoto da ya fito daga kafafen watsa labaran kasar, ya bayyana cewa, ana zargin Peter Mutharika ne da laifuka biyu, da suka hada da ba da shaidar zur, da kuma neman amincewar wasu domin karya doka. Rahoton ya kara da cewa, wadanda ake zargin sun hada kai wajen boye gaskiyar halin da tsohon shugaban kasar ke ciki a lokacin da ya rasu, wato ran 5 ga watan Afrilun bara, tare da yunkurin hana shugaba Joyce Banda damar dorewa mukamin jagorancin kasar, a wancan lokaci da take matsayin mataimakiyar shugaban kasa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China