Bugu da kari, a cewar sabon rahoton da ofishin ya fitar, saboda huldar dake tsakaninsu da kasashe uku da suka fi fama da cutar wato Liberia, Saliyo dakuma Guinea, wasu kasashen da cutar ba ta kai gare su ba, su ma sun gamu da matsaloli da suka shafi raguwar cinikayya, rufe kan iyakokia, soke jadawalin zirga-zirgar jiragen sama, raguwar zuba jari da na sana'ar yawon shakatawa.
Don haka rahoton ya nuna cewa, ya kamata gwamnatocin yammacin kasashen Afirka da hukumomin yankin da abin ya shafa su ci gaba da taimakawa kasashen kan hana sake yaduwar cutar a yankin, kana da sake gina kasa, da kuma daukar matakan da suka hada da inganta ayyukan cibiyoyin lafiya, kafa cibiyoyin yin rigakafi da hana yaduwar cututtuka, kula da harkokin iyakokin dake tsakanin kasashen da kuma kafa tsarin yin rigakafi da daukar matakan gaggawa da dai sauransu. (Maryam)