in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin: Za a zurfafa gyare-gyare a fannin shari'a a shekarar 2015
2015-03-12 17:10:31 cri

A ranar Alhamis din nan ne kotun koli ta jama'ar kasar Sin, da hukumar koli ta gabatar da kararraki ta kasar, suka gabatar da rahoton aiki a majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, inda suka nuna cewa, za su gudanar da gyare-gyare a fannin shari'a a wannan shekara ta 2015, domin samun kyautatuwa da amincewar jama'ar kasa ga fannin shari'a, da kuma inganta adalci cikin ko wace kara da ke gaban kotu.

A safiyar wannan rana ne dai aka gudanar da cikakken zaman taro zageye na uku na majalisar wakilan jama'ar kasa ta Sin karo na 12, inda shugaban kotun kolin kasar Zhou Qiang, da kuma shugaban hukumar gabatar da kararraki a matakin koli Cao Jianming, suka gabatar da rahotanni a madadin sassansu.

Shuwagabannin biyu sun bayyana ci gaban da aka samu a fannin shari'a cikin shekarar da ta gabata, tare da samar da alkaluman kididdigar da abin ya shafa.

Rahoton kotun kolin kasar Sin ta jadadda cewa, gyare-gyaren shari'a ya shiga wani mawuyacin hali a halin yanzu, don haka ya kamata a dauki matakai ba tare da shakku kan ciyar da ayyuka gaba ba. Kaza lika kotun za ta ci gaba da gudanar da harkokin gyare-gyare cikin himma da kwazo, shugaban kotun kolin Zhou Qiang ya jaddada cewa,ya kamata a ciyar da gyare-gyaren tsarin daukaka kara, da tsarin yin rajista gaba, domin warware matsalolin daukaka kara, kuma a zurfafa gyare-gyare kan harkokin gabatar da korafin jama'a, ta hanyar gabatar da wasiku ko zuwa kafa-da-kafa, da ciyar da kafuwar dokokin da suka shafi wannan aiki gaba, sa'an nan a kyautata tsarin ba da diyya kan shari'un da aka yanke ba bisa adalci ba. Kaza lika, a samar da matakan kiyaye ikon lauyoyi wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

Bugu da kari, kamata ya yi a tabbatar da dacewar matakan gyare-gyaren da aka gudanar kan wannan aiki, ta yadda Sinawa za su iya cimma moriya mai gamsarwa bisa gyare-gyaren da aka yi a fannin na shari'a.

Cikin rahoton aiki da hukumar gabatar da kara a kotuna ta gabatar a yayin taron, hukumar ta kuma jaddada zurfafa gyare-gyaren aikinta a shekarar 2015, kana hukumar za ta inganta gyare-gyarenta a fannonin sauke nauyin ayyukan shari'a, da kuma samun tabbaci a fannin tsaron ayyukan ma'aikatan shari'a da dai sauransu, inda shugaban hukumar Cao Jianming ya bayyana cewa,Ya kamata a zurfafa gyare-gyare a fannoni guda hudu wadanda gwamnatin kasar ta Sin ta gabatar, da suka hada da harkokin dake shafar ma'aikatan shari'a bisa bambanbin ayyukansu da dai sauransu, tare da cimma fasahohi masu amfani, na cimma nasarar aikin su a nan gaba.

Kana a ci gaba da aikin gyaran tsarin sa ido kan harkokin shari'a , da kuma mai da hankali kan gudanar da ayyukan daukaka kara kan wadanda suka aikata laifuka ta yin amfani da sana'o'insu, da tsare masu aikata laifuffuka, da kuma haramta wa masu aikafa laifuka yin amfani da kudade, da kadarorinsu da dai sauran ayyukan da suka jibanci kai kara.

Bugu da kari, cikin rahoton da hukumar ta gabatar, ta nuna cewa, tana shirya daukar matakai da dama, na sa ido kan harkokin shari'a a shekarar 2015, kamar fannin sauraron ra'ayoyin hukumomin gabatar da kararraki, game da wasu kararraki masu wuyar shari'a, da kuma neman hanyar binciken kararraki da aka shigar kan manyan laifuffuka tsakanin wurare daban daban.

Bugu da kari, cikin rahotannin da kotun koli, da hukumar gabatar da kararraki ta koli suka gabatar a yayin taron, shuwagabanninsu sun tabbatar da cewa, babban aikin hukumomin biyu a shekarar 2015, zai kasance yanke hukunci ga wadanda suka aikata laifuffukan cin hanci da rashawa yadda ya kamata bisa dokokin kasar.

Don gane hakan, shugaban hukumar gabatar da kararraki ta koli ta kasar Sin Cao Jianming ya ce,A bana, za a mai da hankali kan binciken laifuffukan da shuwagabannin hukumomi, da masu gudanar da muhimman ayyuka suka aikata a yayin da suke gudanar da ayyukansu, musamman ma a wasu hukumomin dake matsayin cibiyar iko, da kudade ko kadarori da dai sauransu.

Kana, cikin rahotannin da suka gabatar, sun bayyana cewa, za su tabbatar da kare hakkin dan Adam, da kuma inganta ka'idar yanke hukunci kan laifukan da ake da shakku game aikata su. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China