An yi cikakken zama karo na 3 na taron shekara-shekara na majalissar wakilan jama'ar kasar Sin a yau Alhamis din nan, domin nazari da tattaunawa, kan rahoton aikin kotun koli ta jama'ar kasar Sin, da na babbar hukumar gabatar da kara ta kasar.
Taron ya samu halartar shugaba Xi Jinping da Firaminista Li Keqiang da shugaban majalisar Zhang Dejiang da kuma sauran shugabannin kasar Sin.
Shugaban kotun kolin jama'ar kasar Sin Zhou Qiang, ya gabatar da rahoto game da manyan ayyuka na shekarar bara, da shirin tafiyar da ayyuka na shekarar 2015 a fannin aikin kotun koli. Har wa yau shugaban babbar hukumar gabatar da kara ta kasar Sin Cao Jianming, shi ma ya gabatar da rahoto game da manyan ayyuka na shekarar bara, da muhimman ayyuka na shekarar 2015 na sashensa. (Lami)