in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan shugabannin kasar Sin sun halarci tarukan wakilan jama'ar kasa na NPC
2015-03-11 09:56:51 cri

A jiya Talata da safe ne, manyan shugabannin kasar Sin suka halarci tarukan wakilan jama'ar kasa na majalisar wakilan jama'ar kasar wato NPC.

Yayin da shugaban zaunannen kwamitin majalisar NPC Zhang Dejiang ya halarci taron wakilan lardin Gansu, ya bayyana cewa, kamata ya yi a ba da muhimmanci kan aikin da zai amfanitar da jama'a da gudanar da ayyukan bada tabbaci da kyautata zaman rayuwar jama'a, da samar da moriya ga jama'a, da warware matsalolin jama'a ta yadda za su ji dadin zaman rayuwa. Kana ya kamata a daidaita dangantakar dake tsakanin aikin raya kasa da yin kwaskwarima da kyautata zaman rayuwar jama'a, da tsara yadda nasarorin da aka samu wajen raya kasa za su amfanawa jama'a, da ci gaba da sa kaimi ga bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma.

Shugaban majalisar bada shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin Yu Zhengsheng ya halarci taron wakilan jihar Ningxia, inda ya jaddada cewa, kamata ya yi a dora muhimmanci kan sha'anin zaman rayuwar jama'a kamar bada ilmi, samar da aikin yi, taimakawa masu fama da talauci, raya kasa tare da kiyaye muhalli da dai sauransu don kyautata zaman rayuwar jama'a daga kalibu daban daban.

Kana ya kamata a bi hanyar Sin mai halayen musamman wajen warware matsalolin da kabilun kasar ke fuskanta, da aiwatar da harkokin addini, da yaki da tsattsauran ra'ayi na addini, da kuma ba da jagoranci ga mabiya  addinai da su tafiyar da harkokinsu, da kyautata zaman rayuwarsu, da kiyaye yanayi mai kyau na addini. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China