in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan shugabannin kasar Sin sun halarci tarukan wakilan jama'ar kasa na NPC
2015-03-10 09:35:16 cri

A jiya Litinin 9 ga wata da safe ne, manyan shugabannin kasar Sin suka halarci tarukan wakilan jama'ar kasa na majalisar wakilan jama'ar kasar wato NPC.

Yayin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron wakilan lardin Jilin, ya yi nuni da cewa, ya

kamata a gudanar da ayyuka ta yadda za su dace da sabon tsarin yau da kullum na bunkasuwar tattalin arzikin kasar, da sa kaimi ga farfado da tsofaffin masana'antu dake yankin arewa maso gabashin kasar, da kara yin hadin gwiwa da mu'amala tare da kasashe da yankunan dake makwabtaka da yankin, da kawar da duk wasu abubuwan da ke kawo cikas ga shirin yin kwaskwarima, da inganta aikin bude kofa ga kasashen waje, da gaggauta zamanintar da aikin gona, da dora muhimmanci kan ayyukan kyautata zaman rayuwar jama'a, da kuma cika alkawarin da aka yi na kawo wa jama'a babban canji da samun moriya.

Yayin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ya halarci taron wakilan lardin Heilongjiang, ya bayyana cewa, ya kamata lardin Heilongjiang ya dukufa wajen warware matsalolin bunkasuwa bisa manyan fannoni hudu. Ya kamata a nemi sabuwar hanyar samun bunkasuwa yayin da ake kiyaye bunkasuwa da kyautata tsari, da farfardo da tsofaffin masana'antu yayin da ake aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a cikin gida, da kuma kara tabbatar da kyautata zaman rayuwar jama'a. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China