A gun taron manema labaru da aka gudanar a yayin taro na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 12, Yin Weimin ya bayyanawa 'yan jarida cewa, kamata ya yi a dauki wasu muhimman matakai don tabbatar cewa, an samar da guraben aikin yi. Na farko shi ne a maida hankali ga daliban da za su kammala karatu daga jami'a, da ci gaba da sa kaimi gare su wajen gina sabbin kamfanoni don samar da guraben aikin yi.
Na biyu shi ne aiwatar da manufar inshorar rasa aiki, da gudanar da aikin sa kaimi ga mutanen da suka rasa aikinsu ta yadda za su sake samun wani aiki.
Na uku shi ne sa kaimi ga sabbin kamfanoni da su kara samar da guraben aikin yi, da kara ilimantar da jama'a game da kafa sabbin kamfannoni, da bada hidima da taimakawa musu wajen warware matsalolin kudi da suke fuskanta.
Na hudu kuwa shi ne a kara bada hidimar samar da aikin yi da horar da masu neman aikin yi. (Zainab)