Mr Zhu ya ce, sakamakon da aka samu wajen raya sabuwar kasar Sin cikin shekaru 60 da suka gabata ya shaida cewa, manufar kabilu ta bai wa kananan kabilu ikon tafiyar da harkokin kansu, kana ta biya bukatunsu na raya tattalin arziki da kyautata zaman rayuwa da kiyaye al'adunsu, kazalika, ta babbatar da dinkuwar kasa daya da hadin gwiwar kabilu daban daban.
Hakazalika kuma, Mr Zhu ya yi nuni da cewa, a gun taron harkokin kabilu na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta Sin da aka gudanar a bara, an kara jaddada ka'idojin yin mu'amala da hadin kai a tsakanin kabilu daban daban, kana an tabbatar da manufofin da abin ya shafa. Ya ce, hadin kan kabilun ba ya nufin kawar da al'adun gargajiya na kananan kabilu ba ne, illa amfana da al'adun musamman a tsakanin kabilun. (Zainab+Lami)