Babban manazarcin cibiyar nazarin ilmin Gabas ta nisa ta kasar Rasha Yakov Berger ya ce, kasar Sin ta samu sakamako na a zo a gani a fannonin tattalin arziki, inganta harkokin zaman rayuwar yau da kullum da al'adu da dai sauransu, lamarin da ya sa, matsayin kasar Sin ya kyautata sosai cikin gamayyar kasa da kasa, da kuma wasu kungiyoyin kasa da kasa, kamar su kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasifik wato APEC, kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO da dai sauransu, kana muhimmancin kasar Sin na ci gaba da karuwa cikin harkokin kiyaye zaman lafiya da kuma bunkasuwar tattalin arzikin duniya
Kaza lika, masanin mai kaifin basira dake taimakawa shugaba kan shawarwarin tafiyar da mulki, kana darektan zartaswa na cibiyar nazarin harkokin shugabanci da dimokuradiyyar nahiyar Afirka Deins Cody ya bayyana cewa, cikin shekarar da ta wuce, kasar Sin ta ba da babbar gudumawa wajen warware matsalolin dake shafar zaman lafiya da tsaro a wasu yankunan Afirka.
Bugu da kari, masaniyar nazarin batun kasar Sin na cibiyar nazarin dangantakar kasa da kasa ta kasar Faransa Alice Ekman ta bayyana cewa, shirin na ziri daya da hanya daya da kasar Sin ta bullo da shi na da ma'ana sosai, wanda ba kawai zai shigar da kamfanonin kasar cikin aikin gina kayayyakin more rayuwa, da kuma inganta bunkasuwar yankunan tsakiya da yammacin kasar ba, haka kuma bisa wannan shiri, za a iya fitar da kayayyakin layoyin jirgin kasa mai sauri zuwa kasashen Turai, a sa'i daya kuma,za a bunkasa hadin gwiwar siyasa da tsaro sakamakon kyautatuwar hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakanin Sin da Turai. (Maryam)