Yanzu haka sojojin kasa na kiyaye zaman lafiya na kasar Sin na kasar Sudan ta Kudu inda za su gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya da rundunar sojan MDD a Sudan ta Kudu.
Hong Lei, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ne ya bayyana haka a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing yau ranar Jumma'a 16 ga wata. Mista Hong ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin ta tura wadannan sojojin kiyaye zaman lafiya a Sudan ta Kudu ne bisa bukatar MDD a hukumance, kuma za su gudanar da aikin kiyaye zaman lafiya a Sudan ta Kudu bisa umurnin MDD. Har wa yau kuma wannan shi ne karo na farko da kasar Sin ta tura sojojinta yankunan da ake yake-yake a kasashen ketare. Bisa iznin da MDD ta ba su wadannan sojojin za su yi aikin taimakawa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a Sudan ta Kudu, tabbatar da tsaron lafiyar fararen hula da goyon bayan kokarin da ake yi na ba da agajin jin kai, bisa umurnin hedkwatar rundunar sojan MDD a Sudan ta Kudu. (Tasallah)