in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
EAC za ta soke shingayen da ba na haraji ba dake kawo cikas ga yawon bude ido
2015-01-14 09:48:18 cri

Gamayyar gabashin Afrika (EAC) na aiki kan soke shingayen da ba na haraji ba dake kawo cikas ga kokarin da ake yi domin mayar da wannan shiyya wani yankin yawon bude ido daya tak.

Sakatare janar na kungiyar EAC, Richard Sezibera, ya yi wadannan kalamai a ranar Talata a lokacin da yake hira tare da manema labarai a cibiyar kasuwancin kungiyar dake birnin Arusha.

A matsayin ofishin sakatariya na EAC, burinmu shi ne ganin shiyyar ta zama wata hedkwatar yawon bude ido daya tak nan zuwa lokacin da ya dace. Kuma wannan ba zai yiyu ba sai idan mun dauki nauyin warware dukkan kalubalolin dake gaban mu, in ji mista Sezibera, tare da bayyana cewa, shirin Visa daya na yawon bude ido ga dukkan shiyyar EAC, tunani ne mai kyau domin tallafawa sana'ar yawon shakatawa a wannan shiyya dake kunshe da manyan wuraren yawon bude ido masu jan hankali sosai. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China