in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fashin baki game da manufar Sin don gane da kare hakkin bil Adama
2015-03-09 15:22:13 cri

A 'yan kwanakin baya ne kasar Sin ta gudanar da wani taro, domin tattauna batutuwan da sauka jibanci babban tsarinta na kare hakkokin bil'adama tsakanin shekarun 2012 zuwa 2015, lamarin da ya ja hankulan daukacin sassan masu ruwa da tsaki.

Idan muka waiwayi tarihi, za mu ga cewa, a watan Agustan shekarar 2012, lokacin da uwargida Hillary Clinton ke matsayin sakatariyar wajen kasar Amurka, ta gabatar da wani jawabi a birnin Dakar, fadar mulkin kasar Senegal. Cikin jawabin nata, Clinton ta bayyana cewa, Amurka na kokarin bunkasa tsarin dimokaradiyya, da kare hakkin bil Adama, a wani mataki na habaka dangantakarta da kasashen nahiyar Afirka.

Clinton ta kuma ja hankalin kasashen Afirka, da su kauracewa hulda da kasashen da ba su da wani buri illa na amfana da nahiyar, ta fuskar tattalin arziki, ba tare da nuna wata damuwa game da kare hakkokin bil'adama ba. Wadannan kalamai na Clinton ko shakka babu tamkar zargi ne ga irin rawar da wasu kasashen ke takawa a Afirka, kuma kowa na iya hasashen kasashen da take yiwa wannan kallo.

Game da wannan batu, a yayin wata ziyarar aiki da ya gudanar a kasar Tanzania, shugaba Xi Jinping na nan kasar Sin ya mai da martani ga wadancan kalamai, yana mai cewa, alakar Sin da kasashen Afirka, alaka ce ta cin moriyar juna, da daidaito da kuma adalci.

Ko shakka babu wannan batu ne da ba ya bukatar wani dogon bayani, alakar Sin da kasashen Afirka ta sabawa irin wadda kasashen yamma ke ra'ayi. Ga misali sau da dama, kasashen yamma su kan manta da bukatun nahiyar ta Afirka, har sai lokacin da aka bukaci taimakon su. A daya hannun kuwa, Sin na taimakawa daukacin nahiyar ta Afirka ba tare da gindaya wani sharadi, ko wata manufa ta siyasa ba. kamar dai yadda shugaba Xi ya bayyana yayin ziyararsa a kasar ta Tanzania.

A wancan lokaci shugaba Xi ya bayyana cewa, Sin na mai da hankali matuka wajen tallafawa kasashen Afirka, a fannonin magance matsalolinsu bisa tsari da ya dace da su, tare da la'akari da manufar girmama 'yancin mulkin kan su, da kimar su, matakin da ya sanya kasashen na Afirka samun ci gaba tare da an tsoma musu baki, cikin harkokinsu na cikin gida ba.

Wani abun lura ma shi ne banbancin dake tsakanin sassan duniya da kasashen yamma, ta fuskar yadda kowa ke kallon batun kare hakkokin bil'adama. Ga misali kasashen Afirka da Sin, na da ma'auni na musamman na ilimi, wanda suke tantance ka'idojin kare hakkin al'umma, yayin da mafi yawan dokokin da kasashen yamma ke amfani da su wajen kare hakkokin bil adama, kan kasance sakamako na dokokin kotuna, da na ikon kowa ya yi abin da yake so. A irin wannan yanayi, mafi yawan dokoki na fitowa daga fassara ko tursasawar kotuna, sau da dama ma gwamnatin na karbar dokokin ne a matsayin tilas. Kuma irin wadannan dokoki cike suke da abubuwa marasa dacewa da martaba hakkokin daidaikun mutane, yayin da wasunsu kan sabawa tsaftacaccen tunani.

A daya hannun kuwa, kasashen Sin da na nahiyar Afirka, sun shafe shekaru aru-aru suna gudanar da rayuwarsu, bisa jigo na musamman na kare hakkokin bil'adama tun daga tushe. Ciki hadda batun tabbatar da kare mutunci da martabar kowa, al'adun da suka kunshi abota, da amincewa juna, da zamantakewa mai inganci, da kuma kare kimar juna, da biyayya ga alkawari irin na zumunci, dabi'u ne da suka zamo tubalin gini na alakar Sin da Afirka, kuma jigo na kare duk wani nau'i na hakkokin bil Adama.

Bugu da kari, wata doka ta ilimi, wadda mashahuran malaman kasar Sin, da masana shari'a suka fitar, ta nuna muhimmancin hada batun kare hakkokin bil'adama da muhimman al'adun al'umma, maimakon dokoki na kotuna. Wato bisa wannan tunani na masana, za a kai ga sauke nauyin kyautata dangantakar kasa da kasa ne kawai, idan an sanya lura kan al'adu, da dabi'u, tare da tarihin siyasar al'umma, cikin mizani na cimma nasarar da aka sanya gaba.

Ana iya cewa, manufar wannan tunani ita ce cimma burin kare hakkokin bil'adama, daga tushen dabi'u da al'adun al'umma tun daga tushe.

Idan mun kalli wannan manufa da kyau, za mu ga ta fi mai da hankali ga amfani da tushen al'adun jama'a, da dabi'unsu, wajen kare hakkokinsu na rayuwa, yayin da sauran ka'idoji na kasa da kasa ke tallafawa cimma nasarar hakan. Kuma ko shakka babu wannan manufa ta amfani da tushe domin samar da ci gaba, ita ce kashin bayan alakar Sin da nahiyar Afirka.

Bisa tarihi, kasashen Afirka da kasar Sin sun fara kulla zumunta ne tun cikin shekarun 1950, inda a wancan lokaci kasar Sin ta rika tallafawa kasashen Afirka wajen samun 'yanci kai daga Turawan mulkin mallaka. Kaza lika kasar Sin ta tallafawa kasashen nahiyar da dama da malaman makarantu wadanda suka rika aiki a yankunan nahiyar, baya ga samar da tallafin karatu ga dalibai 'yan asalin nahiyar ta Afirka. Matakin da ya baiwa dinbin daliban nahiyar samun guraben karatu a jami'o'in dake kasar ta Sin.

Kari kan wannan kasar ta Sin ta samar da taimako mai yawa a fannin kiwon lafiya ga kasashen na Afirka, ciki hadda tura likitocinta, da jami'an jiyya zuwa kasashen nahiyar domin tallafawa marasa lafiya.

A daya bangaren kuma shigar ta nahiyar domin gudanar da harkokin da suka jibanci tattalin arziki da cinikayya, ya taimaka matuka ga bunkasar samar da ababen more rayuwa, da karin guraben ayyukan yi ga al'ummun nahiyar ta Afirka.

Yayin da kasar Sin ke kara bayyana manufofinta ga daukacin duniya, abu ne da ya dace a yaba kwazonta a bangaren kare hakkokin bil Adama. Sai dai hakan ba zai samu ba, har sai ta fadada yayata manufofinta a wannan fanni na kare hakkokin bil'adama, ta yadda duniya za ta kara fahimtar mahangarta game da hakan.

Abu ne da ya dace a yi amfani da cibiyar bunkasa al'adu da kare hakkin bil'Adama ta kasa da kasa mai helkwata a birnin Hague na kasar Netherlands, cibiyar dake kunshe da masana daga kasashe da dama, musamman na Sin da kasashen Afirka, wadanda ke kallon al'adu, da dabi'un al'umma a matsayin ginshikin duk wani aiki, na kare hakkokin bil Adama.

Wannan cibiya za ta iya zamowa madubi dake haskawa duniya, ciki hadda kasashen yamma, mahangar Sin da Afirka don gane da wannan batu na kare hakkokin dan Adam, ta yadda duk mai bukata zai iya nazarta, tare da kara fahimtar hakan ta kyakkyawar mahanga. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China