in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi amfani da sabon dakin gwaji don binciken fasahar rigakafin cutar Ebola
2015-02-04 17:30:43 cri

A kwanakin baya ne aka kammala gina wani sabon dakin gwajin binciken kwayoyin halittu na P4 a birnin Wuhan dake lardin Hubei na kasar Sin, wanda ya kasance daya daga cikin dakunan gwaji mafiya ci gaban fasaha a duniya. Hakan a cewar masanan kasar Sin zai taimaka ga binciken fasahar rigakafin cutar Ebola.

Annobar cutar Ebola wadda take bazuwa musamman ma a nahiyar Afirka da sauran wasu sassan duniya tun daga bara ta sanya al'ummar duniya dandana radadin tasirin wannan cuta mai bazuwa da ke saurin kashe mutum. Sai dai binciken da ake yi kan kwayoyin cutar Ebola na bukatar dakin gwajin kwayoyin halittu mai inganci. A halin yanzu dakin gwaji samfurin P4 ne kawai ke iya samar da kariya ga masu aikin binciken kwayoyin cutar yayin da suke gudanar da aikinsu.

A ranar Asabar da ta gabata ne, aka kammala gina irin wannan dakin gwaji na P4 a birnin Wuhan dake tsakiyar kasar Sin bisa hadin gwiwar kasashen Faransa da Sin, wanda ya kasance irinsa na farko a nahiyar Asiya. Hakan na nufin kasar Sin ta samu damar binciken kwayoyin cuta masu saurin bazuwa. Haka kuma a cewar mista Gao Fu, mataimakin darektan cibiyar rigakafi da shawo kan cututtuka ta kasar Sin, kasar Sin za ta yi amfani da sabon dakin gwajin don gudanar da bincike kan fasahar kandagarkin annobar Ebola.

'Duk da cewa ya zuwa yanzu an gudanar da bincike sosai kan cutar Ebola, amma har yanzu ana bukatar ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi kan yanayin kwayoyin cutar. Har yanzu akwai tambayoyin da ba a amsa ba tukuna.'

Ta hanyar amfani da dakin binciken kwayoyin halittu samfurin P4, za a iya gano yanayin kwayoyin wasu cututtukan da suke iya kashe mutum cikin sauri, wadanda har yanzu ba a gano hanyoyin magance su ba. Wasu cututtuka da su kan barke ba zato ba tsammani kuma babu maganinsu, kamarsu Ebola, da cutar yoyon jini ta Marburg, tilas ne a yi amfani da irin wannan dakin gwaji don gudanar da bincike a kansu. Lokacin da ya tabo batun kafa sabon dakin gwajin a Wuhan, mista Bai Chunli, shugaban cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin, ya ce,

'Kamar yadda ake cewa, kafin a yanka dabba, kamata ya yi a wasa wukar da kyau. Kayayyakin da ake bukata a aikin binciken kimiyya da fasaha sun kasance babban tushen aikin nazarin kimiyya, kuma suke ba da tabbaci ga sakamakon aikin. Haka kuma ingancin kayayyakin shi ke alamanta karfin kasa a fannin kirkiro sabbin fasahohi. Dakin gwaji na P4 da aka gina a birnin Wuhan ya kasance daya daga cikin abubuwan da za su taimakawa kokarin da ake na tabbatar da koshin lafiyar al'ummar kasar Sin, wanda zai taka muhimmiyar rawa a kokarin samar da magungunan rigakafi, da hana bazuwar cutattuka.'

Duk a ranar Asabar, masanan kasashen Sin da Faransa sun yi musayar ra'ayi kan matakan da ake dauka don tinkarar cutar Ebola. Sai dai a cewar mista Gao Fu, mataimakin darektan cibiyar kandagarkin cututtuka, tattaunawar da masanan suke yi ta sheda alamar kawo karshen bazuwar cutar, don haka ana da tabbacin kau da cutar baki daya.

'Yanzu yadda cutar ke bazuwa ya ragu sosai. Don haka mun fara magana kan irin matakan da za a dauka bayan da aka kau da cutar. Kana akwai alamun da suka shaida cewa, ba za a sake samun bullar Ebola a yammacin Afirka ba. Amma akwai yiwuwar a bukaci karin lokaci don jinyar dukkan mutanen da suka kamu da cutar. Dangane da sakamakon da aka samu wajen binciken kwayoyin cutar, yanzu an samu magunguna rigakarin cutar Ebola iri 2, wadanda ake amfani da su wajen kare mutum daga kamuwa da cutar.'

Sai dai Gao Fu ya kara da cewa, bai kamata ba a dakatar da kokarin da ake na bincike game da cutar Ebola, domin har yanzu ba a samu cikakken bayani kan kwayoyin cutar ba.

'Yanayin kwayoyin cutar Ebola yana canzawa.Amma wane irin tasiri canzawar yanayin cutar za ta haifar? Wannan na bukatar a yi nazari kansa a nan gaba.'

Ya zuwa ranar 31 ga watan Janairun bana, alkaluman da aka samu daga ma'aikatar kiwon lafiyar kasar Saliyo sun nuna yadda wadanda suka kamu da cutar Ebola da wadanda suka mutu sakamakon cutar suka karu a kasar. Amma duk da haka, bayan da aka kau da cutar daga kasashen Najeriya da Mali, kana wadanda suke kamuwa da cutar a kasar Laberiya su ma sun ragu, wadannan abubuwa ne da suke nuna alamun yadda aka fara samun nasarar shawo kan cutar a duniya baki daya. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China