in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin da kungiyar AU sun daddale yarjejeniyar karfafa fahimtar juna
2015-01-28 16:22:51 cri

A jiya Talata 27 ga watan nan ne kasar Sin da kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU, suka daddale takardar fahimtar juna a hedkwatar kungiyar AU dake birnin Addis Ababa fadar gwamnatin kasar Habasha. Yarjejeniyar dake da nufin inganta hadin kai tsakanin sassan biyu a fannin bunkasa sufuri, da kuma samar da ababen more rayuwa a nahiyar Afirka.

Shugabar hukumar gudanarwar kungiyar AU uwargida madam Nkosazana Dlamini-Zuma, da manzon musamman na gwamnatin kasar Sin, kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Zhang Ming ne suka sanya hannu kan takardar yarjejeniyar.

Wannan hadin gwiwa dai zai shafi kafa tsare-tsare guda uku, ciki har da samarwa kasashen Afirka layukan dogo na zamani, da tagwayen hanyoyin mota, da kuma bunkasa sufurin sama na yankuna, baya ga habaka harkokin masana'antu.

Idan za a iya tunawa a watan Mayu na shekarar 2014, yayin da firaministan kasar Sin Li Keqiang ke ziyara a kasashen Afirka, ya gabatar da cewa kasar Sin, za ta ci gaba da dora muhimmanci kan raya ababen more rayuwa a kasashen Afrika, a yunkurin ta na karfafa hadin kai da kasashen nahiyar, kana za ta hada kai da kasashen Afrika wajen kafa tsare-tsaren sufurin jiragen kasa, da na mota, da kuma na sama.

Kaza lika Sin na fatan samar da goyon baya ga kasashen nahiyar a fannin bunkasa hada-hadar kudade, da masana'antu, da kuma fasahohi kere-kere.

Bisa kuma wannan yanayin da ake ciki ne, kasar Sin da kungiyar AU suka rattaba hannu kan wannan takardar fahimtar juna a tsakaninsu, game da kafa tsare-tsaren uku, da kuma habaka masana'antun.

Game da hakan wakiliyar bangaren Afirka, kuma shugabar hukumar gudanarwar kungiyar AU Madam uwargida Nkosazana Dlamini-Zuma, ta bayyana cewa, daddale wannan yarjejeniya na da matukar ma'ana. Ta ce,

"A ganin mu, wannan takardar fahimtar juna za ta taimaka, wajen gudanar da yarjejeniyoyi daban daban da aka daddale bisa shirin raya Afirka na shekarar 2063. Muna ganin cewa, daddale wannan yarjejeniya zai samar da moriya ga jama'ar Sin da na kasashen Afirka, kana zai gaggauta dunkulewar Afirka wuri daya. Saboda haka, na yi farin ciki sosai da wannan aiki."

Shi kuwa wakilin bangaren Sin, kuma mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin Zhang Ming, cewa ya yi hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afirka a fannin kafa tsare-tsaren uku, da habaka masana'antun kasashen Afrika, ya dace da yanayin da ake ciki. Zhang Ming ya ce,

"Da farko, tun fil-azal, kasar Sin da kasashen Afirka na gudanar da hadin kai mai karko, kuma suna da fatan ci gaba da hadin kai cikin yakini. Na biyu, kasashen Afirka na cikin wani lokaci na soma samun bunkasuwa a fannin tattalin arziki, wato sun soma samun bunkasuwa a fannonin samar da ababen more rayuwa, da habaka masana'antu. Na uku, kasar Sin ta samu fasahohi sosai kuma tana da babban iko na kafa layukan dogo na zamani, da tagwayen hanyoyin mota, da kuma sufurin sama na yankuna, da kuma fannin habaka masana'antu."

Zhang Ming ya kara bayyana cewa, wannan takardar fahimtar juna ta dace da burin Sin da na Afrika. Ya ce,

"Ana iya cewa, wannan takardar fahimtar juna takarda ce ta karni, batutuwan hadin kai dake cikin ta su na da girma, kuma ta na kara mana kwarin gwiwa, a sa'i daya kuma ta dace da yanayin da ake ciki. Saboda haka akwai yiwuwar tabbatar kudurorin dake kunshe cikin ta. Kungiyar AU ta gabatar da shirin raya kasashen Afrika nan da shekarar 2063, ita ma Sin ta tsara burika biyu na neman ci gaba a shekaru dari. Irin wannan hadin kai ya hada da tsare-tsaren bunkasuwar nahiyar Afrika da Sin, ya kuma kunshi burin al'ummun kasashen Afrika da Sin." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China