in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mata kan manyan mukamai ya karu, in ji rahoton MDD
2015-01-13 14:23:52 cri

Mataimakin kakakin MDD Farhan Haq ya ce, wani sabon bincike na MDD ya ce, kididdiga na nuni da cewar, a cikin shekaru 20 da suka shude, an samu karin yawan mata da ake dauka a ma'aikatu da kamfanoni a kan manyan mukamai a kasashe dabam-dabam na duniya.

Rahoton na MDD ya ce, duk da yake cewar, yawancin hukumomin kamfanoni masu maza zalla suna raguwa, to amma akwai bukatar fafutuka domin tabbatar da cewar, adadin mata ya yi kunnen doki da na maza a kamfanoni.

Haq ya bayyana cewar, hukumar kwadago ta duniya ita ce ta fito da sakamakon sabon binciken wand aka yi wa lakabi da "Mata 'yan kasuwa na samun nasara a Shugabanci", binciken ya yi amfani da bayanai daga kasashe 80 na duniya.

To amma Haq ya ce, duk da wannan ci gaba da aka samu kashi 5 ko kasa da wannan adadi na mata ke shugabantar manyan kamfanoni na duniya, kuma rahoton na nuni da cewar, rawar da mata ke takawa ta haifar da katafaren ci gaba a duniya.

Binciken na nuni da cewar, kasar Jamaica ita ce kan gaba a wajen adadin mata dake rike da manyan mukamai a duniya. Kasar Yemen ita kuma ita ce ta kashe, a bayan sauran kasashe inda kashi 2.1 kawai ne na adadin matan kasar ke rike da manyan mukamai.

Daga cikin jerin kasashen inda mata suka fi samun manyan mukamai, Amurka ita ce kasa ta 15 daga cikin kasashe 108, kuma Britania ita ce ta zanto kasa ta 41. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China