Yancin matan Afrika ya kasance wani muhimmin aiki ga duk wata al'umma domin gaggauta ci gaba mai karko a nahiyar Afrika, in ji wani babban jami'in kungiyar tarayyar Afrika AU a ranar Laraba.
Yancin mata ya zama ginshikin tsarin kawo sauyi ga Afrika, lokaci ya yi da na aiwatar da muhimmin matsayin cewa, mata na iyar rike matsayi a ko wane bangaren zaman rayuwar jama'a domin kyautata karfin yin amfani da albarkatun Afrika, domin moriyar dukkan 'yan Afrika baki daya, in ji Leila Benali Kraiem, darektar sashen ci gaban mata na kwamitin tarayyar Afrika, a yayin wata hirarta tare da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a yayin taron ministocin kungiyar AU a birnin Addis Abeba.
Duk da cewar har yanzu akwai sauran matsalolin dake hana ruwa gudu, matan Afrika sun amfana da wasu matakan yaki da nuna bambanci, in ji madam Kraiem. Mun samu ci gaba sosai wajen samun daidaici tsakanin mabambanta jinsi, amma wannan bai isa ba, ganin cewa mata da 'yan mata har yanzu ba su da damar samun ilimi, kana yi wa mata auren dole da auratarsu yayin shekarunsu ba su kai ba, babban laifi ne domin yana take 'yancin mata, in ji madam Leila Benali Kraiem. (Maman Ada)