Babbar sakatariya a ma'aikatar tsare-tsare da yayata gwamnatin kasar Kenya, Anne Waiguru ta lura da cewa, matan Afrika su ne kashin bayan ci gaban tattalin arziki da zamantakewa tsakanin muhimman mukamai a siyasa, malanta da masana'antu.
A hirarta da Xinhua gabannin babban taron ministocin kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU da za'a gudanar a Adis Ababe na kasar Habasha, Madam Waiguru ta ce, matan Afrika sun shawo kan duk wani kalubale da zai hana su neman ci gaban nahiyar.
A cewarta, Afrika ta samu kyakkyawan ci gaba a bangaren mata cikin shekaru 50 da suka gabata, mata a nahiyar sun karbi damar da aka samar masu, sun kuma zama kashin bayan na habakar nahiyar.
Ministocin Afrika da masana wadanda suka hallara a Adis ababa a ranar Talatan nan sun tattauna ci gaban da kasashe suka yi na rage tazarar da ke tsakanin jinsi a bangarori da suka hada da ilimi, kiwon lafiya, samar da aikin yi, jagoranci da wakilta.
Ta ce, kasashen Afrika da dama sun aiwatar da tsare-tsaren da dokoki da ya rage tazara a tsakanin jinsi. Ga misali, kasar Rwanda ta zama na shida a duniya wajen ragen tazaran jinsi a bangaren ci gaban mata a siyasa a shekarar 2014. Haka kuma kasar Afrika ta Kudu da Senegal sannan Rwandan kuma suna cikin kasashe 10 masu mafiya yawan mata a majalisar dokokinsu.
Anne Waiguru daga nan sai ta yi wa Xinhua bayanin cewa, baya ga rike manyan mukamai a kasa, matan Afrika suna ingiza hauhawar tattalin arziki da zamantakewa a nahiyar, a kasashe kamar Kenya, Ghana da Afrika ta Kudu, mata sun samu ci gaba a kasuwancinsu. (Fatimah)