Mr. Wang wanda ya bayyana hakan yayin taron tattaunawa na kwamitin sulhun MDD na jiya Juma'a, inda aka tattauna kan batun kiyaye hakkokin mata da yara kanana dake yankunan dake fama da rikice-rikice.
Wang Min ya ce, mata suna da muhimmin tasiri a fannin bunkasa zaman lafiya da ci gaba a wasu kasashe da yankunan dake fama da rikice-rikice, don haka ya kamata gamayyar kasashen duniya su mai da hankali game da tasirin mata a fannin dakile tashe-tashen hankula, da kuma batun warware rikice-rikice a kasashen da ke fama da rigingimu.
Har ila yau wakilin na kasar Sin ya yi kira da a mai da hankali kan bukatun mata na musamman, yayin da ake kokarin inganta shigar da su cikin ayyukan sulhu, da shawarwari da dai sauransu. (Maryam)