Jiya Juma'a 27 ga wata, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi kira da a kara bai wa mata damar shiga fagen siyasa da ikon fada-a-ji.
Ban Ki-Moon ya yi wannan tsokaci ne a yayin babban taron shugabanni mata na kasashen duniya karkashin jagorancin hukumar mata ta MDD a Santiago hedkwatar mulkin kasar Chile, wanda ya kuma samu halartar shugabanni da kusoshin mata na fannonin siyasa, tattalin arziki, al'adu daga kasashe fiye da 60.
A yayin bikin bude taron, Ban Ki-moon ya ce, ko da yake dimbin mata na samun damar shiga fagen siyasa, amma a galibi dai, ana bukatar gwamnatoci da zamantakewar al'ummar kasashe daban daban da su kara kokarinsu don kara azama ga aikin neman samun daidaito a tsakanin maza da mata.
An mai da "dora muhimmanci kan mata da hakkinsu don raya wata duniya ta daban" a matsayin babban taken taron. A cikin kwanaki biyu masu zuwa, masu halartar taron za su tattauna kan yadda za a kawar da cikas domin mata su samu matsayin shugabanci, baya ga tattaunawa kan sakamako da darussan da aka samu bisa sa hannu cikin harkokin siyasa da 'yan mata suka yi a cikin shekaru 20 da suka gabata.(Kande Gao)