in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude bikin nune-nunen hotuna game da ci gaban harkokin hakkin dan Adam na kasar Sin a Geneva
2013-10-22 10:54:47 cri

A ranar 21 ga wata da dare, a ofishin M.D.D.dake palace of nations a birnin Geneva, an bude bikin nune-nunen hotuna game da cigaban da aka samu ta fannin raya hakkin dan Adam a kasar Sin, bikin da ofishin kula da harkokin yada labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin da ma'aikatar harkokin wajen kasar suka shirya tare.

A gun bikin, shugaban tawagar kula da taimakawa sauran kasashen duniya wajen tantance hakkin dan Adam na kasar Sin kuma manzon musamman na ma'aikatar kula da harkokin wajen kasar Sin Wu Hailong ya yi jawabin fatan alheri, inda ya ce, girmamawa da kare hakkin dan Adam ya zama babbar ka'idar da gwamantin Sin take bi wajen tafiyar da mulkin kasar. Ya kara da cewa, bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, musamman ma bayan da aka gudanar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje cikin shekaru sama da 30 da suka gabata, tattalin arzikin kasar ya bunkasa da sauri, kuma zaman rayuwar al'umma ya samu kyautatuwa sosai. Baya ga haka, an inganta dokokin raya hakkin dan Adam, kuma jama'a na more hakkin siyasa da 'yanci bisa dokokin kasar.

Wu Hailong ya ce, bisa tushen girmama juna da zaman daidaito da juna, kasar Sin tana fatan inganta mu'amala da sauran kasashe game da raya hakkin dan Adam, a kokarin sa kaimin cigaban hakkin dan Adam na kasar Sin da na sauran kasashen duniya baki daya.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China