Mr. Liu wanda ya bayyana hakan a jiya Jumma'a ya kuma kara da cewa, alakanta ta'addanci da wata kabila, ko wani addini, ba zai haifar da kyakkyawan sakamakon da ake fata ba.
Ya ce a wasu yankunan Afirka, ayyukan ta'addanci na da nasaba da kungiyoyi masu aikata manyan laifuka na kasa da kasa, don haka ya dace a fuskanci yaki da ta'addanci da manufofin da suka dace.
Game da hadin gwiwa a wannan fage kuwa, Mr. Liu ya ce ya zama wajibi gamayyar kasashen duniya su tallafawa kasashen Afirka, a fannin horas da jami'an tsaro, da tsaron iyakoki, da kuma yaki da masu safarar miyagun kwayoyi.
Har wa yau ya ce akwai bukatar maida hankali ga dakile laifukan dake shafar kasa da kasa ta hanyar amfani da fasahar sadarwa.
Wakilin na kasar Sin ya ce a matsayin Sin na kasar da ke yaki da nata nau'in ta'addanci, tana da burin ganin kasashen Afirka sun samu zarafin fuskantar wannan matsala ta irin nasu yanayi, za kuma ta ci gaba da hada kai da su, da ma sauran kasashen duniya, a yunkurin dakile ayyukan ta'addanci, da sauran laifukan da suka shafi kasa da kasa. (Saminu Hassan)