in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu wani karin bayani kan bikin murnar cimma nasarar yaki da hare-haren da sojojin Japan suka yi
2015-01-27 20:37:07 cri
A yau ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana cewa, a halin yanzu, babu wani karin bayani dangane da lokaci da kuma shirye-shiryen bikin murnar cika shekaru 70 na kawo karshen yaki da hare-haren sojojin Japan da kasar Sin ta shirya.

Ta kara da cewa, shekarar bana ita ce cikon shekaru 70 na cimma nasarar yaki da Fascist, shekara ce da ta dace a waiwayi tarihi, da kuma nuna fatan alheri ga makomarmu. Kasar Sin, MDD da wasu kasashen da abin ya shafa za su yi amfani da wannan dama don gudanar da bukukuwa domin koyi da darussa da suka faru a tarihi, da kuma kiyaye zaman lafiya cikin hadin gwiwa, ta yadda za a iya gina wata kyakkyawar makoma mai albarka tare da samar da zaman lafiya a duniya baki daya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China