Sanarwar wadda kafofin yada labarun kasar suka fitar ta yi amfani da garkuwar da aka yi da mutane a birnin Sydney na Australia, a matsayin misali na irin halin da ake ciki game da ayyukan ta'addanci.
Har ila yau sanarwar ta ce sakamakon da aka samu, daga nazari kan hare haren da aka kai a baya, ya nuna cewa 'yan ta'adda sun fi mai da hankali kan kaddamar da farmakin a wuraren cin abinci, da kantuna, da wuraren ibada, da kuma makarantu. Kuma mai yuwuwa ne a samu aukuwar hare-hare a lokutan bukukuwan karshen shekara. Don haka aka tsara ci gaba da wayar da kan jama'a game da hakan, daga yanzu har ya zuwa ranar 19 ga watan Maris na shekara mai zuwa.
Kafar watsa labarun kasar Amurka ta ce majalisar gudanarwa, da jami'an leken asirin Amurka, sun bayyana cewa kawo yanzu, babu wata hakikanin barazana ga Amurkawa 'yan yawon shakatawa, sai dai abinda ya faru a kasar Australiya na garkuwa da mutane a ranar Litinin, alama ce dake nuna yiwuwar hakan.
Kafin wannan gargadi, ba safai gwamnatin Amurkan ke fidda makamanciyar wannan sanarwa ga masu yawon shakatawa ba. Wannan ce dai sanarwa ta farko a bana game da gargadi ga masu yawaon skakatawar.
Kafin hakan a watan Agustar bara, majalisar gudanarwar Amurkan ta taba gargadin Amurkawa game da barazanar aukuwar hare-hare daga kungiyar Al-Qaeda.(Fatima)