in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta Kudu ta musunta jibge sojojin Uganda kan iyakarta da Sudan
2015-03-03 10:44:54 cri

Kasar Sudan ta Kudu ta musunta rahoton dake cewa, za ta jibge sojojin kasar Uganda a kan iyakarta da kasar Sudan, tana mai cewa, babu wassu sojojin a kan iyakarta da Sudan.

Jakadar kasar Sudan ta Kudu a Sudan, Mayan Dot, a cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Khartoum, ya ce, sojojin kasar Uganda suna birane uku ne kawai a kasarta wato Juba, Bor da kuma Bantio.

Rahoton wannan zargin dai ya fito ne daga kamfanin dillancin labarai na kasar ta Sudan wato SUNA, inda ya bayyana cewa, ana shirin jibge sojojin Uganda 16,000 a kan iyakar kasashen biyu.

Sojojin Ugandan dai suna goyon bayan gwamnatin kasar Sudan ta Kudu wajen fada da sojojin adawa na tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar.

Dangantaka tsakanin Khartoum da Kampala ta sha yin tsami yadda Sudan take zargin Uganda da goyon baya tare da boye 'yan tawayen yankin Darfur, da kuma na Revolutionary Front wadanda suke fada da gwamnatin kasar ta Sudan a yankunan Blue Nile da Kudancin Kordofan. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China