A sabon zagaye na tattaunawa tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta Kudu game da rabon kan iyaka ya sake cin tura inda aka tashi ba tare da wani ci gaba mai armashi ba, in ji wani jami'in kasar Sudan.
Abdalla Al-Sadiq, shugaban kwamitin rabon kan iyaka na kasar Sudan ya shaida wa manema labarai a birnin Khartoum cewa, an yi ta mai da hankali ne a kan batutuwan da aka riga aka amince da su a tarukan baya, babu wani sabon abu da aka tattauna.
Bangarorin biyu sun kammala taron kwanaki 5 a Adis Ababa, babban birnin kasar Habasha ba tare da wani sakamakon a zo a gani ba, amma sun amince su kafa wata tawagar musamman da za ta kula da warware batutuwa da suka shafi rabon kan iyaka na kasashen biyu.
Batun kan iyaka na daga cikin manyan matsalolin dake kawo cikas wajen warware banbancin dake tsakanin kasashen na Sudan da Sudan ta Kudu, wanda ya kawo takaddama a kan kan iyakokin 5 da suka hada da mai arzikin man fetur na Abyei, Dabatal-Fakhar, Jabel Al Migainis, Samaha da Kafia Kanji. (Fatimah)