Rahotannin daga bangaren sojin Sudan ta Kudu na cewa, 'yan tawaye na tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar sun yi luguden wuta a birnin Bantio dake jihar Unity mai arzikin man fetur, abin da ya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma.
Yan tawayen sun afkawa birnin Bantio ne a ranar Talata, sannan suka afka wa birnin Al-Nasir, inda suka kai hari a kan wani sansanin sojin gwamnati dake unguwar Obodo a masarautar Al-Shuluk a jihar Upper Nile, in ji kakakin sojin kasar.
Kakakin ya yi bayanin cewar, wannan ne karo na hudu da magoya bayan Riek Machar ke kai irin wannan harin cikin makonni biyu, abin da ke nunawa karara cewar, an saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma.
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit da jagoran 'yan tawayen Riek Machar sun rattaba hannu a kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta a ranar 2 ga watan nan da muke ciki na Fabrairu, wanda ya tabbatar da tsagaita bude wuta, raba iko da kafa gwamnatin rikon kwarya, da fatan kuma za'a kawo karshen tashin hankalin da ake fuskanta nan da 5 ga watan gobe na Maris.
Babban mai shiga tsakani na kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afrika IGAD Seyoum Mesfin tun da farko ya sanar da cewar, ana sa ran bangarorin biyu su rattaba hannu a kan yarjejeniyar karshe a ranar 20 ga wannan watan na Fabrairu. (Fatimah)