Dakarun sojin kundumbala 144 na kasar Sin da za su yi aiki cikin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD, sun tashi daga birnin Jinan zuwa kasar Sudan ta Kudu ta jirgin saman musamman na MDD.
Yayin bikin ban kwana da su karkashin jagorancin shugaban reshen sojojin kasa na kiyaye zaman lafiya Wang Zhen, sojojin sun rera taken kasa, sannan sun jaddada aniyyarsu game da cimma burin kiyaye zaman lafiya a karkashin tutar kasar Sin.
Ana sa rana da isar su Sudan ta Kudun, dakarun na Sin za su fara ayyukan binciken yanayin kasar, da kafa sansanin soja, da karbar na'urorin soja da kuma sauran ayyuka.
Rahotanni sun ce sauran sojoji da jami'ai 520 na reshen sojojin kasa masu aikin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin, za su isa kasar ta Sudan ta Kudu a lokuta daban daban. (Lami)