in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta kiyasta 'yan gudun hijirar Sudan ta Kudu dubu 121 dake Sudan
2015-03-03 10:59:53 cri

Ma'aikatar daidaita harkokin jin kai (OCHA) ta MDD ta kiyasta cewa, a cikin watan Febrairu, 'yan gudun hijirar kasar Sudan ta Kudu 121 400 ke kasar Sudan.

A ranar 19 ga watan Febrairu, an kiyasta adadin 'yan gudun hijirar kasar Sudan ta Kudu 121 400 da suka shiga kasar Sudan sakamakon barkewar tashe tashen hankalin a Sudan ta Kudu a cikin tsakiyar watan Disamban shekarar 2013, in ji OCHA a cikin wani rahoton da aka fitar a ranar Litinin. An kai daukin taimakon jin kai, musammun ma na abinci ga 'yan kasar Sudan ta Kudu dake gudun hijira a kasar Sudan, in ji wannan rahoto, tare da jaddada cewa, har yanzu babu isassun kudaden tafiyar da wadannan ayyukan jin kai.

Kasar Sudan ta Kudu ta fada cikin mawuyacin hali da rikici a cikin watan Disamban shekarar 2013 a yayin da fada ya barke tsakanin sojojin dake biyayya ga shugaba Salva Kiir da dakarun dake karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasa Riek Machar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China