Wani jami'in tsaro na kasar Iraki ya bayyana cewa, sojojin kasar sun kai farmaki ga birnin Dour na jihar Salahudin dake arewacin kasar a jiya Lahadi, kuma suna shirya murkushe dakarun kungiyar IS da suka yi kaka gida a wannan jiha.
Wannan jami'i ya kara da cewa, sojojin Iraki sun yi amfani da tankunan yaki da manyan boma-bomai da rokoki masu cin gajeran zango, a yayin da suke kai farmaki kan birnin Dour dake da nisan kilomita 150 daga birnin Bagadaza da kuma yankunan dake dab da shi, abin da ya yi sanadiyyar lalata gine-gine da dama. Sabo da jerin farmaki da kuma gargadin daukar matakan soja ya sa galibin mazaunan wurin suka tsere daga gidajensu. A halin yanzu kuma, babu kowa a cikin wannan birni. A sa'i daya kuma, wani reshen sojojin Iraki yana kan hanyar zuwa birnin Tuz-Khurmato na jihar Salahudin, domin yanke hanyar jigilar kayayyaki na dakarun dake wurin, tare da yi musu kawanya.
A wannan rana, shugaban hukumar tsaron jihar Salahudin Sheikh Jasim al-Jbarra ya ce, firaministan kasar Iraki Haider al-Abad ya sanar a daren wannan rana a birnin Samarra dake arewacin kasar cewa, an fara daukar manyan matakan soja a hukunce kan dakarun kungiyar IS a jihar Salahudin.(Lami)