Rahotanni daga kasar Iraqi na nuna cewa, fiye da mayakan kungiyar IS 70 ne aka hallaka a ranar Lahadi lokacin wata arangama tsakanin su da sojojin Iraqi da Kurdawa wadanda jirgin saman yakin na Amurka ke jagora, in ji wani jami'in tsaro.
Arangamar ta faru ne da tsakar rana lokacin da mayakan kungiyar da dama suka far ma kauyen Sultan Abdaullah a kan babban hanyar garuruwan Gwer da Qaiyara a kudancin birnin Mosul mai tazaran kilomita 400 daga Bagadaza.
Mayakan kungiyar ta IS sun kwace kauyen, amma jiragen saman yaki karkashin jagorancin na Amurka sun yi luguden wuta, sannan jami'an tsaro suka afkawa sansanin 'yan kungiyar da motocin yaki da igwa.
Rundunar tsaron gwamnati sun ga gawawwaki fiye da 70 na mayakan kungiyar a warwatse a wuraren da aka yi luguden wutan da kuma bakin iyakan kauyukan wanda ake kyautata zaton cewa, daya daga cikin shugabannin su Taha al-Afri na cikin wadanda suka mutu.
Haka kuma biyu daga cikin jami'an tsaron bangaren Kurdawa da ake kira Peshmerga sun mutu, sannan wassu guda biyar suka ji rauni a lokacin arangamar. (Fatimah)